A wani kudirin doka da ministan harkokin wajen kasar Nijar ta dauka ta dakatar da ayyukn kungiyar ta ICRC wacce a karkashin kungiyar akwai kungiyoyi irin su Red Cross da dai sauran su tare da rufe dukkan wurarensu da ke cikin kasar Nijar nan take.
Matakin da Emoud Issouf na M62 ya ce ya yi dai dai
Sai dai wasu ‘yan Nijar na nuna damuwa dangane da abin da suka kira illar da ke tattare da wannan matakin da zai raba daruruwan ‘yan Nijar da aiki da kuma duban ‘yan kasar da taimakon da su ke samu daga wannan kungiyar.
Gwamanatin Nijar dai ba ta bayyana dalillan da suka sanya ta dakatar da ayyukan kungiyar ICRC ba, saboda haka ne kungiyoyin fararen hula irin su malam Abdou Mohamed ke ganin akwai bukatar gwamnatin ta fito ta yi wa ‘yan kasa bayani game da dalilin ta na daukar wannan matakin kan wannan kungiyar.
Kawo yanzu dai kungiyar ta ICRC ba ta ce komai ba akan wannan matakin da gwamnatin Nijar ta dauka, sai-dai gwamnatin ta sha alwashin ci gaba da gudanar da bincike a kan ayyukan kungiyoyi ma su zaman kansu na ciki da wajen kasar domin daukar mataki a kan duk wacce aka samu tana tafiyar da aikinta ba a kan ka’idar sabuwar tafiyar da Nijar ta sa a gaba ba.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna