Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farmakin Sojojin Mu Ya Fatattaki ISIS A Somalia-Shugaba Trump


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kai farmakin a ranar Asabar a shafukan sada zumunta, yana mai bayyana lamarin da auna "Babban mai shirya kai hari na ISIS da sauran 'yan ta'addan da ya dauka kuma yake jagoranta."

Jiragen yakin Amurka sun kai hari kan kungiyar IS da ke Somaliya, inda suka kai farmaki kan abin da jami'ai suka bayyana a matsayin tungar manyan jami'an kungiyar a yanki mai tsaunuka.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kai farmakin na ranar Asabar a shafukan sada zumunta, yana mai bayyana lamarin da auna "Babban mai shirya kai hari na ISIS da sauran 'yan ta'addan da ya dauka kuma yake jagoranta."

"Wadannan masu kisa da muka samu suna boye a cikin kogo, suna yi barazana ga Amurka da kawayenmu," in ji Trump, "Hare-haren sun lalata kogon da suke ciki, sun kuma kashe 'yan ta'adda da dama ba tare da cutar da fararen hula ba."

Wata sanarwa ta daban daga sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ta ce hare-haren sun afkawa wani yanki ne a tsaunin Golis na Somalia, kuma "ya kara kassara karfin ISIS na kulla makirci da kai hare-haren ta'addanci da ke barazana ga 'yan Amurka, abokanmu, da fararen hula da basu san hawa basu san sauka ba."

Tsakanin Trump da Hegseth babu wanda ya ambaci sunan mai shiryawa IS dabarun kai harin, sai dai jami’an Amurka sun ce an kai farmakin ne a wani aikin hadin gwiwa da gwamnatin tarayyar Somalia.

Janar Adnan Abdi Hashi, kwamandan rundunar Puntland Devish ya ce hare hare ta saman sun auna akalla wasu wurare 10 da mayakan IS suke a Cal-Miskaad, wanda wani bangare ne na tsaunukan Golis.

“ Ko shakka babu hare haren sun auna akalla wurare 10 a nan Cal-Miskaad, inda galibi koguna ne, kuma mun yi imanin cewa mun kashe mayakan da dama,” in ji janar din.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG