A yau Litinin Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi fatali da kalaman Donald Trump na cewar Afirka ta kudu na kwace filaye inda yace a shirye ya ke ya yi wa takwaransa na Amurka bayani game da manufar sauye-sauyen gwamnatinsa ke yi a kan filaye.
Da alama dai kalaman Trump na tsokaci ne a kan dokar karbe filayen jama’a domin amfanin gwamnati da Ramaphosa ya rattabawa hannu a watan da ya gabata wacce ta shar’anta cewa gwamnati na iya, a wasu lokutan ko yanayi, “kin biyan diyya” a kan filayen data yi niyyar karbewa domin amfanin al’umma.
Malakar kasa batu ne da ke yawan janyo takaddama a Afrika ta Kudu, inda farar fata ke ci gaba da mallake galibin gonakin kasar shekaru 30 bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.
Duk kokarin magance wannan rashin daidaito na janyo suka daga masu ra’ayin rikau, ciki har da Elon Musk haifeffan Afrika ta Kudu, attajiri mafi karfin arziki a duniya, wanda ke da karfin fada a ji cikin mashawartan Trump.
“Babu filin da gwamnatin Arika ta Kudu ta kwace,” kamar yadda Ramaphosa ya bayyana a cikin wata sanarwa bayan ikirarin na Trump inda nan ma ya zargi gwamnatin da musgunawa wani rukunin mutane tare da barazanar dakatar da tallafa kasar da kudade.
“Muna sa ran tattaunawa da gwamnatin Trump game da manufar sauye-sauyenmu a kan filaye da kuma batutuwa na alakar kasa da kasa,” a cewar sanarwar.
“Muna da tabbacin cewa daga wannan tattaunawa, za muyi musayar fahimta game da wadannan batutuwa.”
Dandalin Mu Tattauna