Wani uba a kasar Pakistan ya hallaka ‘yarsa budurwa bayan data dora hotunan bidiyon da yake ganin basu dace ba a dandalin sada zumunta na Tiktok, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a yau Alhamis.
Mutumin bai jima da dawo da iyalansa gida daga kasar Amurka ba domin su zauna a birnin Quetta dake yankin kudu maso yammacin Pakistan, a cewar babban jami’in ‘yan sandan yankin, Babar Baloch.
Uban wanda yake a tsare, yayi ikrarin cewar ya harbe ‘yarsa a farkon makon da muke ciki bayan data ki daina shigar banza da dora hotunan da iyalin ke ganin basu dace ba a dandalin na Tiktok, a cewar Baloch.
‘Yan sanda na daukar lamarin da abinda ake kira da kisan ‘ya mace da wani daga cikin dangi ke yi domin gudun abin kunya.
Dangi na jini sun hallaka kimanin mata 1000 a Pakistan a bisa hujjar cewar suna kokarin kare mutuncin iyalinsu ne, a cewar hukumar kare hakkin ‘yan adam ta Pakistan (HRCP).
Dandalin Mu Tattauna