Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin jinkirta aikin sakin Falasdinawa fursunoni domin musayar Yahudawa 3 da aka saki tunda fari a musayar baya-bayan nan ta yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza, kamar yadda ofishinsa ya bayyana,
“Firai Minista Benjamin Netanyahu da ministan tsaronsa Isreal Katz, sun bada umarnin jinkirta sakin ‘yan ta’addar da aka tsara yi yau har sai batun sakin mutanenmu da ake garkuwa dasu cikin lumana a gabobin yarjejeniyar masu zuwa ya tabbata,” kamar yadda ofishin Netanyahu ya bayyana.
Wata majiyar Hamas ta shaidawa AFP cewar kungiyar na tattaunawa da masu shiga tsakani domin matsa wa Isra’ila lamba ta saki fursunoni 110 da ya kamata a saki a yau Alhamis.
Kokarin Karfafa Yarjejeniyar
A jiya Laraba jakadan Amurka a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, ya gana da Fraiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da nufin kara karfi ga yar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ilan da mayakan Hamas a Gaza, bayan shafe sama da watanni 15 ana bata kashi.
Daga bisa, Witkoff wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen saisaita yarjejeniyar ta makonni 6, ya duba wata hanya mai fadin kilomita 6 dake kewayen Gaza, inda ma’aikatan samar da tsaron da Amurka ta dauka haya ke sa ido kan dawowar Palasdinawan da aka daidaita komowa gidajen su.
Witkoff shine jami’in Amurka mafi girman mukami daya ziyarci Gaza a cikin shekaru.
Witkoff ya shaidawa kafar labarum Fox a makon jiya, Shirin shi na ziyartar hanyar Philadelphi dake kusa da kan iyakar Gaza da Masar.
Dandalin Mu Tattauna