Mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da haka ga maneman labaran fadar shugaban kasa a yau Laraba a fadar ta Aso Villa, dake Abuja.
Ministan ya tattaro tawagar masu bincike na musamman karkashin jagorancin babbar sakatariya a ma’aikatar cikin gidan, Dr. Magdalene Ajani, domin su bincika wadannan zarge-zarge tare da gabatar da cikakken rahoto a kai.
Lagbaja ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron lakca kan mutumin daya fi fice a shekarar 2024 mai taken, “rawa da gudunmowar rundunar sojin Najeriya ga cigaban kasa”, wacce cibiyar nazarin zaman lafiya da mahimman fannonin ilimi, na jami’ar Ilori ta shirya.
A yau Laraba Majalisar Dattawan Najeriya ta tabattar da ai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya
Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar barayin daji wadanda ke satar mutane don neman kudin fansa.
Isra’ila ta ce daya daga cikin hare-haren da ta kai a yankunan kudancin birnin Beirut ya kashe Ibrahim Muhammad Kobeisi, wanda Isra’ila ta bayyana a matsayin babban kwandan sojojin Hezbollah da ke sa ido kan tsarin makamai masu linzami na Hezbollah.
Yayin da yake jawabi a gaban taron, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ya ce, lokaci ya yi da za a sharewa Afirka hawayenta kan wannan bukata.
Al’amarin ya hada da wani kwale-kwale dake dauke da fasinjoji wanda ya nutse a cikin ruwan ambaliya, abinda yayi sanadiyar mutuwar wasu mata 4.
Ministan Tsaron Najeriya Abubakar Badaru ne ya gabatar da bukatar a taron kolin da aka yi kan makomar duniya yayin karo na 79 na babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya dake gudana a birnin New York, na Amurka.
A wata hira ta musamman da Bloomberg, hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya tattauna kalubale da matakan da suka dauka dangane da kaddamar da matatarsa, wadda ita ce mafi girma a Afirka.
Daga cikin wadanda aka kashe a hare-haren har da yara 35 da mata 58, a cewar jami'an Lafiyar Lebanon.
A ranar Lahadi, hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Edo, nasarar da PDP ta ke kalubalanta.
Domin Kari
No media source currently available