Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Minista Ya Bada Umarnin Bincike Kan Zargin Cin Hanci A Hukumar Gidan Gyaran Hali


Ministan Cikin Gida, Olubunmi Olatunji-Ojo
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Olatunji-Ojo

Ministan ya tattaro tawagar masu bincike na musamman karkashin jagorancin babbar sakatariya a ma’aikatar cikin gidan, Dr. Magdalene Ajani, domin su bincika wadannan zarge-zarge tare da gabatar da cikakken rahoto a kai.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo,ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike ba tare da gindaya sharuda ba kan zargin almundahana a hukumar kula da gidajen gyaran halin Najeriya.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yau Laraba, hadimin ministan mai kula da harkokin yada labarai, Babatunde Alao, yace da kakkausar murya yayi allawadai da dabi’ar da ake zargin aikatawa.

“Ma’aikatarmu ba za ta lamunci wata tawaya akan muradanmu na asali na rikon amana da gaskiya da kiyaye dukiyar al’umma. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen magance cin hanci da rashawa tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a haka ya fuskanci fushin hukuma, “ a cewar Tunji-Ojo.

An ruwaito cewa Ministan ya tattaro tawagar masu bincike na musamman karkashin jagorancin babbar sakatariya a ma’aikatar cikin gidan, Dr. Magdalene Ajani, domin su bincika wadannan zarge-zarge tare da gabatar da cikakken rahoto a kai.

Binciken ya biyo bayan zargin cin hancin da Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya yi a cikin wani faifan bidiyo da wani mai gudanar da jaridar intanet, Martins Otse da aka fi sani da Verydarkman, ya saki akan wani babban jami’in hukumar gyaran halin Najeriya.

A faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta, Bobrisky ya kuma yi zargin baiwa jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) cin hancin Naira miliyan 15 domin su daina tuhumarsa da laifin halasta kudaden haram.

Da yake martani a sanarwar da ya fitar a jiya Talata, shugaban sashen yada labarai na EFCC, Dele Oyewale, yace shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya kafa tawagar masu bincike domin gudanar da binciken kwakwaf a kan batun.

Bayan shafe watanni 6 a gidan kaso, an sako Bobrisky daga gidan yarin Kirikiri a ranar 5 ga watan Agustan da ya gabata.

A watan Afrilun da ya gabata wata babbar kotun tarayya dake Legas ta aike da Bobrisky zuwa kurkuku ba tare da zabin tara ba sakamakon amsa laifin cin zarafin takardar Naira da hukumar EFCC ta tuhume shi da aikatawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG