Hukumar samar da shingen kare hamada ta ce aikin nan na dasa bishiyoyi tsawon kilomita 1500 a jihohi 11 na arewacin Najeriya domi yaki da hamada na samun nasara.
Sanata George Akume yace gwamnatin Shugaba Tinubu na sane kuma ta na tausayawa ‘yan Najeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, don haka aka takaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.
Babban darktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana tsananin lamarin a sanarwar da ya fitar.
Yayin ganawan sun tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi tsaro a yankin Afirka ta yamma da harkar bada agaji da kuma rawar da Najeriya ke takawa a fannin bada gudunmowa tsakanin kasa da kasa.
A watan Yulin da ya gabata, Ministan Ilmi Tahir Mamman yace daga shekarar 2025, ba za a sake kyale daliban da basu kai shekaru 18 da haihuwa ba su rubuta jarrabawar kammala sakandare (SSCE).
'Yan sandan jihar Zamfara sun yi faretin wani Jam'in Civil Defense da ke yi wa 'yan bindiga safarar makamai, Likitan jabu, da matan manyan 'yan bindiga cikin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka
Rikicin kabilanci tsakanin Fulani da kabilun Gomon ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
Bikin mika takardar shaidar cin zaben ya gudana ne a shelkwatar INEC dake Abuja a yau Alhamis.
Da take zartar da hukuncin, alkaliyar tace dukkanin shaidun da lauyoyin masu kara suka gabatar sun samesu da laifi.
Al'umar jihar Zamfara sun fara kokawa akan ce-ce ku-cen da ake yi tsakanin gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da karamin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Bello Muhammad Matawalle.
Domin Kari
No media source currently available