Sojojin Najeriya 3 da jami'an 'yan sanda 4 suka hallaka yayin da suke kokarin dakile harin 'yan bindiga akan babbar hanyar Zamfara a yau Alhamis.
Shari’ar wacce ta ja hankula da dama, ta samo asali ne daga gazawar Ruth Auta ta baiwa jaririnta kulawar da ta dace yayin da take aikin kwana a asibitin Royal Bolton.
Mutanen da aka dawo da su daga Hadaddiyar Daular Larabawan sun hada mata 90 da maza 310.
Harin da rundunar sojin saman Najeriya ta kai a karamar hukumar Shiroron jihar Neja ya hallaka fiye da ‘yan ta’adda 28.
Duk da cewar PDP da dan takararta a zaben, Mr. Asue Ighodalo, basu sa hannu akan yarjejeniyar ba, sauran jam’iyyu ciki harda APC da dan takararta, Monday Okpebholo da takwaransa na jam’iyyar Labour, Olumide Akpata, sun rattaba hannu akanta.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a jiya laraba a fadar shugaban Najeriya dake Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, yace an tura karin jami’ai musamman ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin domin su bude hanyar.
Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) Ezekiel Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “adadin wadanda suka mutu ya kai mutum 30”,
Ga dukkan alamau har yanzu akwai sauran rina a kaba game da batun wanzuwar man fetur a Najeriya da kuma arhar shi duk da shigowar matatar man Dangote cikin harkar.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya tabbatar da karbar tallafin kudade naira biliyan 3 daga gwamnatin tarayya da za a yi amfani dasu wajen warware kalubalen da ambaliyar ruwa ta haifar.
Domin Kari
No media source currently available