Wadanda aka kaman sun hada da, wani gungun batagari mai mambobi 7 da ake zargin ‘yan fashi da makamin da suka tare matafiyan dake safarar atamfofi da yaduddukan da aka kiyasta kudinsu zai kai Naira miliyan 4.
Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ce ta bayyana wadannan alkaluma a rahoton da ta fitar a jiya Alhamis.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta rufe kasuwar magani ta Gomboru dake birnin Maidugurin jihar Borno, inda aka wanke tare da shanya gurbatattun magunguna a rana domin sake sayar dasu ga jama’a sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta afkawa jihar.
Wadanda umarnin ya tsame sun hada da, kafafen yada labaran da aka tantance da jami’an zabe da motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan bada agajin gaggawa.
Shugaban kasar ya roki ‘yan takarar gwamnan da jam’iyun siyasa da magoya bayansu dasu mutunta tsarin dimokiradiya da kuma zabin mutane.
Jami’an tsaro na ci gaba da samun galaba a yaki da ‘yan bindigar da suke addabar jihar Zamfara, inda suke dada kama su, da tarwatsa yunkurin su na Kai hare hare, da hana satar mutane da sauran munanan hare-hare.
Mista Sam Olumekun, Kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayani da Ilimin Zabe na INEC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis bayan taron shugabannin hukumar.
Masu lura da al'amura na cewa, zaben zai iya zama zakaran gwajin dafi ga farin jinin gwamnatin APC mai mulki a jihar ta Edo da ma matakin tarayya.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rushe kwamitocin rikon kananan hukumomin jihar 44.
A cewar mataimaki na musamman ga shugaban a kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, Tinubu na so ya zauna a gida domin magance matsalolin dake addabar Najeriya.
Ragin ya biyo bayan gabatar da harajin da aka yi a farkon shekarar nan me cike da cece-kuce, al’amarin daya gamu da turjiya daga kungiyoyin kwadagon NLC da TUC da kuma masu hulda da banki.
Wani zauren zantawa kan lamuran yau da kullum mai taken “CONNECT THE DOTS” ya karfafa cewa hadin kan matasa da jagorori zai kawo raguwar tabarbarewar tsaro musamman a arewacin Najeriya.
Domin Kari
No media source currently available