Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tsaron Najeriya Na Fama Da Karancin Dakaru - Lagbaja


Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Lagbaja ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron lakca kan mutumin daya fi fice a shekarar 2024 mai taken, “rawa da gudunmowar rundunar sojin Najeriya ga cigaban kasa”, wacce cibiyar nazarin zaman lafiya da mahimman fannonin ilimi, na jami’ar Ilori ta shirya.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukaci kowane dan Najeriya ya shigo a dama da shi a harkar tsaron lafiya dukiyoyin al’ummar kasa a maimakon barin hakan a hannun hukumomin tsaro.

Lagbaja wanda ya samu wakilcin babban hafsa mai kula da horaswa a rundunar, Manjo Janar Sani Gambo Muhammad, yace ba abu ne mai yiyuwa ba ga jami’an tsaro milyan 2 su iya tsare al’ummar Najeriya fiye da mutum miliyan 200.

Babban hafsan sojan, wanda yace gwamnatin Najeriya na da niyyar daukar karin sojoji kamar yadda ta yi alkawari, ya jaddada cewa rundunar sojin kasar, da sauran hukumomin tsaro, na fama da karancin dakaru.

Ya kuma bayyana matsalolin rashin wadatattun kudi da ma’aikata da kayan aiki da kuma gurguwar fahimtar da ‘yan Najeriya suka yiwa harkar tsaro a matsayin abubuwan dake tarnaki ga ayyukan rundunar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG