Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya kara farashin na litar mai.
“An yi kone-kone, kuma har bam ma ya tashi. Wasu suna cewa mutum 80 wasu na cewa ya kai 100 mutanen da aka kashe.”
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta rahotanni dake cewa Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ce ta umarci kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sayar da litar man akan naira dubu daya.
“Da zarar mun kammala wasu tsare-tsare da kamfanin NNPCL, man mu zai fara shiga kasuwa.”
Wasu rahotanni sun ce farashin litar a wasu manyan biranen kasar ya kai har 925 zuwa 1,000.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta ba da tukwici mai tsoka ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga kama mutanen.
Matatar man Dangote ta Najeriya ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan, in ji wani jami'in gudanarwa a ranar Litinin kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
A ranar Litinin ne Najeriya ta tuhumi wasu mutane 10 da laifin cin amanar kasa da kuma hada baki wajen tunzura sojoji su ta da kayar baya, bayan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar a watan da ya gabata, inda dubban mutane suka fantsama kan tituna domin nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa.
Sanarwa ta kara da cewa, ana tuhumar Sonnberger, wacce 'yar kabilar Igbo ce da ke zaune a Canada da laifin furta kalamai na barazana.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da nadin Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya a matsayin sabon sarkin masarautar Ningi na 16 a kan mataki, Sarki mai daraja ta 1.
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya tabbatar da cewa ya na fuskantar matsalar kudi sakamakon tsadar man fetur na manyan injuna (PMS), lamarin da ke kawo cikas ga dorewar ayyukan samar da man.
Domin Kari
No media source currently available