A cewar alkaluman kididdigar farashin sayen kayayyaki da NBS ta fitar, ma’aunin auna jumlar hauhawar farashin ya ragu zuwa kaso 32.15 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata.
A cewar NEMA, jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya, Salem Alshamsi, ne ya mika kayan agajin ga hukumomin Najeriya a filin saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Lahadi tace, Shugaba Tinubu ya bukaci al’ummar Musulmi suyi amfani da wannan lokaci wajen sake nazari kan kyawawan halaye da koyarwa ta Annabi Muhammad (S.A.W).
Mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan a yau litinin cikin wata sanarwa.
Bidiyon ya nuna yadda matar Abbas Haruna mai suna Hussaina ta zayyana irin halin da mijinta ya shiga bayan da ya samu sabani da shugaban bataliyarsa lamarin da ta ce ya kai ga tsare shi har ma ya haukace.
Sai dai a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar a ranar 15 ga watan Satumbar 2024, Ribadu ya nemi Aziegbemi da ya janye kalaman nasa inda ya kwatanta lamarin a matsayin “zuki ta malle”
A wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar ya ce ya sayarwa da kamfanin NNPCL da man fetur din da kudin dalar Amurka ba da Naira ba.
Sanarwar ta kara da cewa, Obansanjo ya kai makamanciyar ziyarar ga Sarkin Benin Esama of Benin, Chief Gabriel Igbinedion, wanda shi kuma ya cika shekaru 90 don taya sa murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Lamarin ya faru ne kusan watanni biyu bayan wani yunkurin hallaka Trump a wani gangamin yakin neman zabe a jihar Pennsylvania.
Wasu fitattun malaman addinin Islama daga Najeriya sun yi kira ga 'yan Afrika mazauna Turai da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin sauraran wa’azi daga bakin maluman a taron da aka saba gudanarwa shekara-shekara a Turai a kan muhimmancin zamantakewa mai kyau.
Domin Kari
No media source currently available