Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Na Bukatar Kujeru Na Dindindin A Kwamitin Tsaro Na MDD - Shettima


Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima

Yayin da yake jawabi a gaban taron, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ya ce, lokaci ya yi da za a sharewa Afirka hawayenta kan wannan bukata.

Najeriya ta bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka wajen kira da a samarwa da nahiyar kujeru na dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Yayin da yake jawabi a gaban taron a ranar Talata, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ya ce, lokaci ya yi da za a sharewa Afirka hawayenta kan wannan bukata.

Shugabannin duniya sun hallara a birnin New York inda za su kwashe kwanaki hudu ana tattauna wa kan matsaloli da suka addabi duniya a taron wanda ake yi a karo na 79.

Dangane da matsalar tsaro da ke addabar wasu kasashen nahiyar, musamman Najeriya, Shettima ya kara da cewa kasashen Afirka sun tashi tsaye wajen shawo kan matsalolin na tsaro.

“Muna hada kai wajen ganin mun dakile wannan barazana ta tsaro. Babban taron da Najeriya ta jagoranta na kasashen Afirka don yaki da ayyukan ta’adanci a watan Afrilun da ya gabata, ya nuna alamun za a samu nasara a yakin da ake yi da ta’addanci.”

Kazalika ya tabo batun rikicin Isra’ila da Hamas inda ya nuna cewa kasashen duniya sun gaza wajen shawo kan rikicin yana mai nuni da cewa samar da kasashe biyu shi ne mafita ga rikicin da ake fama da shi a yankin.

Baya ga wadannan batutuwa, mataimakin shugaban na Najeriya ya kuma nuna irin illa da sauyin yanayi yake yi a yankunan Afirka inda ya buga misali da ambaliyar ruwan da ta mamaye jihar Bornon Najeriya a makonnin da suka gabata.

Ya kara da cewa akwai bukatar kasashen su tashi tsaye su hada kai wajen shawon matsalar ta sauyin yanayi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG