Hukumomin tsaro sun bayyana cewa bude wutar da aka yi a wata babbar sakandare a jihar Georgia ta Amurka a jiya Laraba, ya hallaka akalla mutane 4 tare da raunata wasu 9.
Kwamitin kolin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki tare da janye abinda ya kira da karin farashin man fetur 'maras dalili'.
A cewar Shugaba Xi, za a bada fiye da rabin adadin kudaden a matsayin bashi, inda za a zuba dala biliyan 11 “cikin nau’ukan tallafi daban-daban” sannan a bayar da dala biliyan 10 ta hanyar karfafa gwiwar kamfanonin China su zuba jari.
Gwamnatin tarayyar Najeriya da kasar China sun amince da kulla kawance wajen yakar laifuffukan da suka shafi kudi da halasta kudaden haram da kuma daukar nauyin ta’addanci.
Ana tsare da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 9 a kurkukun Kuje bayan da aka tuhumesu da laifin cin amanar kasa yayin da kotun ta ba da umarnin tsare mace daya tilo daga cikinsu a gidan gyaran hali na Suleja.
Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya MAN, ta ce karin kudin man fetur da aka yi zai iya haddasa tashin farashin kayayyaki a kasar.
Kungiyar gwamnonin ta bukaci shugabannin hukumomin tsaron Najeriya su dauki mataki akan barazanar da Wike ke yi, ta hura wutar rikici a jihohin kasancewar babu wanda ya fi karfin doka a kasar.
NLC ta ce wannan tamkar cin amanar yarjejeniyar karin mafi karancin albashi ne zuwa Naira 70,000.
Masanan sun yi kiran ne bayan isar Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle da Hafsoshin sojin Najeriya Sokoto don yakar 'yan ta'adda.
Taron da aka yi a makon jiya a nan Yamai a tsakanin Hafsan Hafsoshin Nijar da takwaransa na Najeriya na daga cikin nasarori masu nasaba da ayyukan tuntubar da jakadan Najeriya Mohammed Sani Usman ya gudanar a kokarin farfado da hulda a tsakanin kasarsa da Nijar.
Bill Gates na martani ne a kan tambayar da aka yi masa game da dabarun da gwamnatin tarayyar Najeriya ka iya dauka wajen ba da tallafin makudan kudade a harkar kiwon lafiya.
Al'ummar jihar Sakwato sunyaba da umarnin da shugaba Tinubu Yayiwa Ma'aikatar Tsaro Na Su Tare Yankin Arewa Maso Yamma Don Kawo Karshen Tsaro.
Domin Kari
No media source currently available