Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Ta Kai Sabbin Hare-hare A Lebanon


Yakin Isra'ila da mayakan Hezbollah
Yakin Isra'ila da mayakan Hezbollah

Isra’ila ta ce daya daga cikin hare-haren da ta kai a yankunan kudancin birnin Beirut ya kashe Ibrahim Muhammad Kobeisi, wanda Isra’ila ta bayyana a matsayin babban kwandan sojojin Hezbollah da ke sa ido kan tsarin makamai masu linzami na Hezbollah.

Yayin da babban taron na Majalisar DinkinDuniya ke gudana, Isra’ila ta kara yin lugudan wuta a kan mayakan kungiyar Hezbullah da ta take ta auna su a kasar Lebanon ranar Talata, inda adadin wadanda suka mutu a hare-haren ta sama tun daga ranar Litinin da ta wuce ya karu zuwa 564, yayin da wasu 1,835 suka jikkata.

A jimullance, Isra’ila ta ce ta kai hari a wurare 1,600, inda jami’an kiwon lafiya na Lebanon suka ce an kashe yara 50 a wurare daban daban, tare da mata akalla 94.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce hare-haren da ta kai a ranar Talata ya shafi wurare da dama da ta auna na kungiyar Hezbullah, ciki har da mayakan da ke da hannu wajen harba rokoki da dama a arewacin Isira’ila.

Isra’ila ta ce daya daga cikin hare-haren da ta kai a yankunan kudancin birnin Beirut ya kashe Ibrahim Muhammad Kobeisi, wanda Isra’ila ta bayyana a matsayin babban kwandan sojojin Hezbollah da ke sa ido kan tsarin makamai masu linzami na kungiyar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG