Matsayar EFCC ta ci karo da ta ofishin yada labaran Yahaya Bello dake cewar tsohon gwamnan ya mutunta gayyatar hukumar.
A bisa kididdigar da ake da ita, tsarin tattalin arzikin halal na duniya na da jarin daya kai dala tiriliyan 7 kuma ana hasashen cewar zai bunkasa da dala 7.7 kan nan da 2025.
A jiya Talata, gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi al’ummar kasar game da ruwan da za’a saki daga madatsar lagdo dake kasar kamaru.
A yau Laraba aka ce tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta yi masa.
A 'yan kwanakin nan, rahotanni na cewa Cardoso na fuskantar suka saboda rashin iya shawo kan kalubalen tattalin arziki da kuma daidaita darajar Naira.
Babban hafsan sojin kasar Oumar Diarra ya ce sojoji sun yi nasarar kashe maharan, amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Wata sanarwa da Kakakin rundunar Manjo Stephen Nantip Zhakom ya fitar a ranar Talata ta ce an kama makaman ne a wani same da aka kai a karamar hukumar Jos ta arewa a jihar.
Kantoman karamar hukumar Bukkuyum, Nasiru Muhammad, wanda ya ba da tabbacin faruwar lamarin yace, an samu hatsarin ne saboda lodi fiye da kima, da rashin hakuri.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana yakinin cewar nan bada jimawa ba ta’addancin da kasurgumin dan ta’addan nan daya jima yana aikatawa a jihar da kwayenta zai zo karshe.
Sanarwar ta kara da cewa ana cigaba da kula da sanya idanu akan wasu mutane su kimanin 100.
Wannan matakan sun biyo bayan fashewar madatsar ruwan Alau da ke jihar Borno da ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya.
A cewar NEMA, kawo yanzu an gano gawawwakin fasinjoji 9, sannan ana cigaba da gudanar da aikin ceto.
Domin Kari
No media source currently available