Ana tsare da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 9 a kurkukun Kuje bayan da aka tuhumesu da laifin cin amanar kasa yayin da kotun ta ba da umarnin tsare mace daya tilo daga cikinsu a gidan gyaran hali na Suleja.
Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya MAN, ta ce karin kudin man fetur da aka yi zai iya haddasa tashin farashin kayayyaki a kasar.
Kungiyar gwamnonin ta bukaci shugabannin hukumomin tsaron Najeriya su dauki mataki akan barazanar da Wike ke yi, ta hura wutar rikici a jihohin kasancewar babu wanda ya fi karfin doka a kasar.
NLC ta ce wannan tamkar cin amanar yarjejeniyar karin mafi karancin albashi ne zuwa Naira 70,000.
Masanan sun yi kiran ne bayan isar Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle da Hafsoshin sojin Najeriya Sokoto don yakar 'yan ta'adda.
Taron da aka yi a makon jiya a nan Yamai a tsakanin Hafsan Hafsoshin Nijar da takwaransa na Najeriya na daga cikin nasarori masu nasaba da ayyukan tuntubar da jakadan Najeriya Mohammed Sani Usman ya gudanar a kokarin farfado da hulda a tsakanin kasarsa da Nijar.
Bill Gates na martani ne a kan tambayar da aka yi masa game da dabarun da gwamnatin tarayyar Najeriya ka iya dauka wajen ba da tallafin makudan kudade a harkar kiwon lafiya.
Al'ummar jihar Sakwato sunyaba da umarnin da shugaba Tinubu Yayiwa Ma'aikatar Tsaro Na Su Tare Yankin Arewa Maso Yamma Don Kawo Karshen Tsaro.
A jihar Borno kuma, ambaliyar ta yi barna a kananan hukumomi da dama sannan ta lalata gonaki da yanzu an wakilta wata tawaga ta musamman da aka dorawa alhakin bibiyar al’amuran ambaliyar a jihar ta Borno.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya kara farashin na litar mai.
“An yi kone-kone, kuma har bam ma ya tashi. Wasu suna cewa mutum 80 wasu na cewa ya kai 100 mutanen da aka kashe.”
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta rahotanni dake cewa Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ce ta umarci kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sayar da litar man akan naira dubu daya.
Domin Kari
No media source currently available