Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga Ba Gudu Ba Ja Da Baya – ‘Yan Najeriya


Nigeria Police Protest
Nigeria Police Protest

“A yadda ‘yan bindiga suke ta addabar jama’a a Zamfara, Sokoto da Katsina, me ya sa hukumomin tsaro ba su iya gano masu yin wadannan ayukan ba, sai yanzu da mutane suka fito za su yi zanga-zanga akan wahalar da ke damunsu ne suka iya bincike?”

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana kudurinsu na soma zanga-zanga a duk fadin kasar kan tsananin rayuwa da suke fuskanta, duk kuwa da gargadin da hukumomin tsaron kasar suka bayar kan yiwuwar rikidewarta zuwa tarzoma.

‘Yan Najeriyar da ke kukan rashin kyakkyawan shugabanci da ya haifar da kuncin rayuwa, tsadar abinci da kayayyaki, da kuma rashin tsaro, sun tsara gudanar da zanga-zangar lumana a duk fadin kasar, domin kira ga gwamnati da ta sauya wasu manufofin ta da ake ganin su suka jefa ‘yan kasar a cikin halin da suke ciki.

To sai dai hukumomin tsaron kasar sun yi ta ba da gargadin yiwuwar rikidewar zanga-zangar zuwa tashin hankali.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Najeriyar, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, ya ce duk da yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka shata somawa a ranar 1 ga watan Agusta, kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a kasar Kenya.

'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya

Ita ma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS, cewa ta yi ta gano wasu jagororin zanga-zangar da “manufarsu ita ce tumbuke gwamnati.” A kan haka ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kauracewa shiga zanga-zangar da kuma duk wani nau’i na tashin hankali.

Ko bayan wannan kuma an ruwaito wasu gwamnonin jihohi da kuma Ministan babban birnin tarayya Abuja, suna gargadi tare bayyana shirinsu na hana zanga-zangar a yankunan su.

To sai dai duk da haka, wasu ‘yan Najeriyar sun dage kan cewa zanga-zanga ba gudu ba ja da baya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wasu ‘yan kasar na cewa ba wata barazana da za ta hana su ‘yancinsu na gudanar da zanga-zangar lumana, domin nuna fushinsu kan matsanancin halin da suke ciki.

Masu wannan ra’ayin na cewa duk gargadin da gwamnati da hukumoninta ke yi na tashin rikici sakamakon zanga-zangar, “barazana ce kawai da kuma yunkurin kawar da hankalin ‘yan Najeriya kan mawuyacin halin da suka jefa jama’a a ciki.”

Wani daga cikin jagororin zanga-zangar ta Najeriya, Ambasada Abdul Danbature, ya fadawa wakilin Muryar Amurka cewa “muna kan bakan mu gaskiya. Zanga-zanga za mu yi ta in Allah Ya yarda, ba gudu ba ja da baya.”

Shi kuwa dan fafutuka kuma masani shari’a da tsarin mulki, Deji Adeyanju, martani ya mayar wa hukumomin tsaron kasar, musamman kan ikirarinsu na cewa sun gano makarkashiyar yin amfani da zanga-zangar domin ta da rikici.

Yace “a yadda ‘yan bindiga suke ta addabar jama’a a Zamfara, Sokoto da Katsina, me ya sa ba su iya gano masu yin wadannan ayukan ba, sai yanzu da mutane suka fito za su yi zanga-zanga akan wahalar da ke damunsu ne suka iya bincike?”

Adeyanju ya kara da cewa “an taba yin zanga-zangar lumana ta rikide zuwa tashin hankali in ba gwamnati ce ta ke tura wasu don su ta da hankali ba?

Lauyan ya kuma gargadi sojoji da sauran jami’an tsaro da kada su shiga hurumin da ba na su ba. “An taba ganin inda (a tsarin dimokaradiyya) soja ko DSS za su gayawa jama’a abin da za su yi da abin da ba za su yi ba?

“Ai kundin tsarin mulkin kasa ne ya bai wa 'yan kasa ‘yanci na su yi zanga-zanga in suna ganin cewa akwai wani abu da ba ya tafiya daidai. Shin al’umma za ta bi tanadin kundin tsarin mulki ne ko kuwa umarnin DSS ko soja?” in ji lauya Adeyanju.

Ab tsara soma zanga-zangar ne a ranar 1 ga wata mai zuwa na Agusta a duk fadin Najeriyar.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG