Shugaban Kasa Bola Tinubu ya roki ‘yan Najeriya dasu jingine shirin zanga-zangar nan mai taken a “endbadgovernance” a turance da aka tsara gudanarwa a wata mai zuwa.
Ministan Yada Labarai, Muhammad Idris, wanda ya yiwa wasu zababbun maneman labaran fadar shugaban kasa jawabi a yau Talata, yace Tinubu ya bukaci masu shirya zanga-zangar dasu jingine shirin tare da sauraron martanin shugaban kasar akan korafe-korafensu.
A cewar ministan, “kan batun shirin zanga-zanga, shugaban kasa bai ga dalilin yin haka ba. Ya bukacesu su jingine shirin. Ya bukacesu suyi dakon martanin gwamnatinsa akan korafe-korafensu.
An shirya gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa, dake kara kankama a shafukan sada zumunta, a ilahirin jihohin najeriya da babban birnin tarayya, Abuja, a watan Agusta mai kamawa.
Har yanzu ba’a san ko su wanene jagororin zanga-zangar ba.
Farashin kayayyakin abinci dana masarufi sun yi tashin gwauron zabi a watannin baya-bayan nan, a yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsalolin hauhawar farashi da matsin tattalin arzikin da tagwayen manufofin gwamnati na janye tallafin man fetur da hade kasuwannin musayar kudade a wuri guda suka janyo.
Dandalin Mu Tattauna