Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Wata Sabuwar Kokoluwa


Kasuwar 12 mile dake birnin Lagos.
Kasuwar 12 mile dake birnin Lagos.

Hasashen hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a duk shekara ya kai wata sabuwar kokoluwa na shekaru 28, da ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna ranar Asabar.

Hasashen hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a duk shekara ya kai wata sabuwar kokoluwa na shekaru 28, da ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna ranar Asabar, lamarin da ya kara tsananta wahalhalun da ke kara tabarbarewar al’umma kan sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu.

A dai dai wata na 18 ne hauhawar farashin kayayyaki ya tashi daga kashi 33.69 cikin 100 a wata daya da ya gabata.

Matsalolin tashin farashin ya taso ne sakamakon sauye-sauyen da Tinubu ya yi, inda aka yi ta rage tallafin man fetur da wutar lantarki da kuma rage darajar kudin Naira sau biyu a cikin shekara guda.

Kungiyoyin Kwadago, wadanda suka dakatar da yajin aikin da suka kira neman a kara musu sabon mafi karancin albashi, sun yi zargin cewa sauye-sauyen na cutar da talakawa, tare da jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa a cikin shekaru da dama da suka gabata.

Bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta wallafa sun nuna cewa abinci da abubuwan sha da ba na barasa ba, sun ci gaba da zama mafi girma wajen haifar da hauhawar farashin kayayyaki a watan Mayu.

Hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya haifar da mafi yawan tashin farashin kayayyaki a Najeriya, ya tashi zuwa kashi 40.66 cikin 100 daga kashi 40.53 cikin 100 a watan da ya gabata.

Masu fashin baki sun ce hauhawar farashin kayan abinci da karancin Naira ne, ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Babban bankin kasar ya kara kudin ruwa a watan Mayu a karo na uku a wannan shekara, sakamakon karuwar hauhawar farashin kayayyaki.

Gwamna Olayemi Cardoso na Babban Bankin Najeriya ya nuna cewa Karin kudin ruwan da aka yi zai tsaya tsayin daka har tsawon lokacin da ya dace don kawo faduwar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG