Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yi Fatali Da Matakan Da Aka Dauka Wurin Nada Sarki Sanusi


Masarautar Kano
Masarautar Kano

Hukuncin kotun na yau Alhamis ya rushe ko soke sanya hannu akan dokar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar da majalisar ta kammala aikinta akan daftarin dokar

Babbar kotun tarayya dake Kano ta soke dukkanin aikace-aikacen da gwamnatin Kano tayi bayan majalisar dokokin jihar Kano tayi wasu sauye-sauye a kundin dokar kula da harkokin masarautu ta jihar a watan jiya, Mayu.

Hukuncin kotun na yau Alhamis ya rushe ko soke sanya hannu akan dokar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar da majalisar ta kammala aikinta akan daftarin dokar, da sake nada sarkin Kano Muhammadu Sanusi akan karagar sarautar Kano da kuma raka shi zuwa gidan sarkin Kano da jami’an gwamnati sukayi.

A zaman kotun karkashin jagorancin mai shari’a AM Liman, ya umarci dukkanin bangarorin da wannan shari’a ta shafa su koma matsayin su na baya, wato gabanin ya bada odar kotun ta baya, zuwa lokacin da zai kammala sauraron wannan batu na takaddamar sarautar Kano.

Wannan na nufi a koma lokacin da ake da sarakuna biyar da masarautu biyar a jihar Kano.

Sai dai alkalin ya karbi korafin lauyoyin wadanda akayi kara na dakatar da ci gaba da shari’ar har sai kotun daukaka kara ta saurari korafin su kan hukunci da shi mai shari’a AM Liman ya zartar cewa, kotun tarayya nada hurumin sauraron wannan batu na takaddamar sarauta a jihar Kano.

Dukkanin matakai da hukunce-hukuncen da kotun ta zartar sun biyo bayan karar da daya daga cikin masu nadin Sarki a fadar Kano Alhaji Aminu Babba DanAgundi ya shigar yana kalubalantar matakin gwamnatin jihar Kano dangane da batun.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG