Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Za Ta Fuskanci Karin Rashin Wutar Lantarki


Kasuwar Makola dake kasar Ghana.
Kasuwar Makola dake kasar Ghana.

Al'ummar Ghana da tuni suka fusata su ke kokawa kan daukewar wutar lantarki ba tare da shiri ba, sun sake fuskantar karin zullumi bayan da masu rarraba wutar lantarkin suka sanar da karin katsewar wutar lantarki a makonni masu zuwa.

Daukewar wutar lantarki da aka fi sani da “dumsor” a yaren Akan na Ghana, na kara jefa al’umma cikin wahalar gudanar da harkokin kasuwanci da tuni ke kan gwiwarsa saboda matsalar tattalin arzikin kasar - mafi muni cikin shekaru goma.

A ranar Alhamis, kamfanin Ghana Grid da Kamfanin Wutar Lantarki da ke rarraba wutar lantarki a fadin kasar, da ke da yawan mutane miliyan 33 a yammacin Afirka, sun ce za a shafe makwanni uku ana samun matsalar wuta saboda aikin gyaran da ake na samar da iskar gas a Najeriya.

Najeriya dai na baiwa Ghana kaso na iskar gas da take bukata, domin samun makamashi ga cibiyoyin wutar lantarkin kasar.

Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan kamfanin WAPco mai kula da bututun mai da ke shigar da iskar gas daga Najeriya, ya kuma yi gargadin cewa za a samu raguwar yawan iskar gas da ake da shi saboda aikin gyaran da ake yi a Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG