Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOKOTO: Mahara Sun Kashe Mutane 5 Ranar Sallah


Wasu masallata suna sallah a Masallaci
Wasu masallata suna sallah a Masallaci

Mahara sun kashe mutane biyar, su ka yi garkuwa da hudu, su ka kuma raunata wadansu mutane biyar a harin ta'addanci da suka kai a jihar Sakkwato ranar Sallah.

Lamarin dai ya faru ne a garin Tudun Doki na karamar hukumar Gwadabawa dake gabashin Sakkwato, a arewa maso yammacin Najeriya.

Garin na Tudun Doki, gari ne da ya hada Hausawa da fulani zaune wuri daya, kuma Fulanin ne suka soma jin karar harbe-harben kafin kowa ya ankara, a cewar Kantoman karamar Hukumar Muhktar Bello Abdulrahman.

'Yan'uwan wasu daga cikin wadanda 'yan ta'adda su ka kashe a yayin da su ke ibada a Kano.
'Yan'uwan wasu daga cikin wadanda 'yan ta'adda su ka kashe a yayin da su ke ibada a Kano.

Zama irin na Hausawa da Fulani wuri daya zama ne wanda duk lokacin da aka samu harin ta'addanci, za'a rika kallon kallo, kuma a kan haka ne Kantoman karamar hukumar yace suka zauna da jama'ar yankunan suka tattauna.

Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta hannun kakakin ta a Sakkwato ASP Ahmad Rufa'i ta tabbatar da mutuwar mutane shida, sanadin wannan harin, sai dai yace suna ci gaba da bincike a kan batun.

Wannan lamarin dai yana faruwa ne a daidai lokacin da daruruwan jama'ar da ayyukan ta'addanci suka raba da muhallansu, ke ci gaba da fuskantar kalubalen rayuwa.

Gwamnatin jihar Sakkwato kamar takwarorin ta na jihohin arewa maso yamma na ci gaba da daukar matakan shawo kan wannan matsalar ta ayyukan 'yan bindiga, sai dai lamarin na ci gaba da wanzuwa a wasu wurare.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

Mahara Sun Kashe Mutane 5 Ranar Sallah
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG