Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Rukunin ‘Yan Majalisar Wakilai Ya Gabatar Da Tayin Wa’adin Shekaru 6 Ga Shugaban Kasa Da Gwamnoni


Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

‘Yan majalisar karkashin jagoranci Ikenga Ugochinyere mai wakiltar mazabar tarayya ta Ideato, sun gabatar da tayin wa’adin mulkin shekaru 6 falan 1 ga shugaban kasa da gwamnoni jihohin najeriya 36.

A yau Litinin, wani rukunin ‘yan Majalisar Wakilai ya bada shawarar yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima, abinda suka hakikance cewar zai inganta tsarin shugabanci a kasar.

‘Yan majalisar karkashin jagoranci Ikenga Ugochinyere mai wakiltar mazabar tarayya ta Ideato, sun gabatar da tayin wa’adin mulkin shekaru 6 falan 1 ga shugaban kasa da gwamnoni jihohin najeriya 36.

Haka kuma, rukunin ‘yan majalisar ya bukaci a kirkiri ofishoshin mataimakin shugaban kasa guda 2, daya daga yankin kudanci sannan daya daga yankin arewacin kasar.

Ikenga Ugochinyere mai wakiltar mazabar tarayya ta Ideato,
Ikenga Ugochinyere mai wakiltar mazabar tarayya ta Ideato,

A cewarsu, mataimakin shugaban kasa na farko zai zamo wanda zai iya gadon kujerar shugaban kasa, a yayin da mataimakin na 2 zai kasance ministan kula da tattalin arziki, kuma dukkaninsu 2 zasu kasance ministoci.

Haka Kuma, ‘yan majalisar sun bada shawarar yin gyara a dokar zaben 2020 domin tabbatar da cewar an gudanar da ilahirin zaben gwamnoni a rana guda.

Rukunin daya kunshi kimanin ‘yan majalisa 30 ya kuma bada shawarar yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya domin bada damar yin karba-karba a sha’anin shugabancin kasa tsakanin yankunan mulkin kasar guda 6 domin tabbatar da daidaito a sha’anin wakilci tare da rage hakilon neman kirkirar sabbin jihohi.

Sauran shawarwarin ‘yan majalisar sun hada da: gyaran kundin tsarin mulki domin bada damar shugaban kasa da mataimakinsa na 1 su fito daga yankin kasa guda (kudu ko arewa) kuma mataimaki na 1 shine zai gaje kujerar shugaban kasar idan har ya samu larurar da zata iya hana shi mulki, don haka mataimakin shugaba na 1 (shine mai gado), shi kuma na 2 (shi zai kula da harkokin gudanarwa da tattalin arziki).

Rukunin mai lakabin, ‘yan majalisa masu ra’ayin sauyi, yace shawarwarinsa akan kudire-kudiren kawo sauyi a fagen siyasa da harkar zabe wadanda suka tsallake karatu na 1 zasu taimaka wajen rage yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati da yakukukan neman zabe da hada kan kasa da tabbatar da sauyin gwamnati cikin sauki da dorewa da samar da cigaba mara tsaiko da adalci da raba daidai da ‘yancin gashin kan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)da sarrafa kudaden gwamnati yadda ya dace da magance matsalar ‘yan uwa da dangi a harkar gwamnati dama matsalar magudi a harkar zabe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG