Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hajjin Bana: Maniyyata Miliyan Daya Da Dubu Dari Biyu Sun Isa Saudiyya


Thousands of Muslim pilgrims make their way to throw stones at a pillar
Thousands of Muslim pilgrims make their way to throw stones at a pillar

Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah ya sanar da zuwan maniyyatan kusan miliyan daya da dubu dari biyu daga sassa daban-daban na duniya.

A wani taron manema labarai da gwamnati ta gudanar a birnin Riyadh, ya tabbatar da cewa alhazan sun iso cikin kwanciyar hankali, kuma suna cikin koshin lafiya.

Al-Rabiah ya bayyana jajircewar Saudiyya na yin hidima ga “baƙin Allah.”

Ya yi nuni da irin gagarumin kokarin da shugabannin kasar ke yi, na saukaka zuwan maniyyata zuwa masallatai biyu masu tsarki da ma sauran wurare masu tsarki.

Muslim worshipers pray around the Kaaba, Islam's holiest shrine, at the Grand Mosque in Saudi Arabia's holy city of Mecca, June 4, 2024 as pilgrims arrive ahead of the annual hajj pilgrimage.
Muslim worshipers pray around the Kaaba, Islam's holiest shrine, at the Grand Mosque in Saudi Arabia's holy city of Mecca, June 4, 2024 as pilgrims arrive ahead of the annual hajj pilgrimage.

"Muna tabbatar da cewa mahajjata za su iya gudanar da ayyukansu cikin sauki da kwanciyar hankali yayin samun kulawa," in ji shi.

Al-Rabiah ya jaddada wajabcin bin ka'idoji da umarni, don tabbatar da ingantattun hidimomi ga dukkan mahajjata.

Ya yi nuni da wani sabon kamfen na kasa da kasa da aka kaddamar, da nufin wayar da kan jama’a kan illar da ke tattare da saba ka’idojin aikin Hajji, da fadawa hannun masu damfara ta yanar gizo.

Ya ce yakin ya shafi kasashe sama da 20 a duniya. Bugu da kari, kamfen na kasa "Babu Hajji ba tare da izini ba," wanda Ma'aikatar Cikin Gida da Masarautar yankin Makka ke jagoranta, na neman ilmantarwa da aiwatar da ka'idojin shirya aikin Hajji.

Ya bayyana hakan ne domin tabbatar da cewa dukkan mahajjata sun kammala ibadarsu cikin jin kwanciyar hankali da tsari.

Aikin Hajji ya kunshi yin dawafi da yin salloli a Dutsen Arafat da "jifan Shaidan" da sauransu.

Aikin Hajji kuma yana cikin shika-shikan Musulunci kuma wajibi ne kowane Musulmi da ya samu iko ya gudanar da shi akalla sau daya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG