Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Tarar “Multichoice” Naira Miliyan 150, Tare Da Umartarsa Ya Baiwa ‘Yan Najeriya Damar Kallon Shirye-Shiryensa Kyauta Tsawon Wata Guda


COURT
COURT

Kwamitin alkalai 3 karkashin jagorancin Thomas Okusu ne ya zartar da hukuncin a yau Juma’a.

Kotun Kula da Kasuwanci da Kare Hakkin Mai Sayen Kaya ta Najeriya taci tarar reshen kasar na fitaccen kamfanin sayar da shirye-shiryen talabijin, “Multichoice”, mamallakin kafafen DSTV da GOTV, naira miliyan 150 saboda yin jayayya akan hurumin kotun tare da umartarsa daya baiwa ‘yan Najeriya damar cin gajiyar shirye-shiryensa kyauta tsawon wata guda.

Kwamitin alkalai 3 karkashin jagorancin Thomas Okusu ne ya zartar da hukuncin a yau Juma’a.

A baya can kotun ta hana Multichoice kara kudin kallon shirye-shiryensa ba tare da sanarwa ba, bisa la’akari da karar da lauya Festus Onifade ya shigar wanda yayi ikrarin cewar sanarwar karin kudin ta kwanaki 8 bata wadatar ba.

Onifade yayi karar DSTV, inda ya zargi kafar da zalunci wajen yin karin kudi ba tare da bada sanarwar wata guda ga abokan huldarsa ba inda yayi amfani da damar wajen samun umarnin wucin gadi daga kotu.

Lauyan kamfanin Multichoice ya ce hukunce-hukuncen baya sun yi maganin batun daidiata farashi, a yayin da Onifade ya maida hankalinsa akan rashin bada wadatacciyar sanarwa a maimakon karin kudin, abinda ya sabbaba kotun tabbatar da huruminta tare da zartar da hukunci akan kamfanin Multichoice.

Daga bisani kotun ta tsayar da ranar 3 ga watan Yuli domin sauraron cikakkiyar karar da bangaren masu kara ya shigar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG