Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro Na Cigaba Da Ta'azzara a Jihar Sokoto


Yan bindiga
Yan bindiga

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da tunzura jama'a a Najeriya har wasu na ganin da ma an mayar da su makwabciyar kasar in har Najeriya ba ta iya kula da kare rayukan su.

Wannan na zuwa ne lokacin da mahukunta ke cewa suna samun nasara ga yaki da ta'addanci, kuma suna kan daukar matakai na kawar da matsalar baki daya.

Da dadewa al'ummomi na arewacin Najeriya ke kokawa kan matsalar rashin tsaro, kuma kawo yanzu matsalar na cigaba da addabar wasu wurare, duk da matakan da mahukunta ke cewa suna dauka tun daga gwamnatin da ta gabata har zuwa wannan mai ci.

Yankin gabashin Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin yankunan da har yanzu matsalar ta ki ja da baya musamman a Isa da Sabon birni, duk da ikirarin da gwamnati ke yi cewa ana samun saukin matsalar.

Muhammad Abdullahi Gobir yace su har yanzu ba su ga sauki ba.

Shi ma wani mazuanin kauyen Tarah, Kwamred Hassan Tarah yace suna neman sauki ne kawai daga Allah, domin tura ta kai bango.

Wannan yanayin ne ya sa har wasu ke ganin da ma an mayar da su a Jamhuriyar Nijar tunda Najeriya ta kasa kula da samar mu su tsaro.

A nata haujin gwamnatin jihar Sakkwato tace ta dauki matakai kuma sun fara yin akiba, kamar farfadowa da biyan kudin alawus ga jami'an tsaro dake bakin daga, samar da motoci, kafa rundunar tsaro, har ma an samu ceto wasu mutane fiye da 250 da aka yi garkuwa da su, a cewar mataimaki na musamman ga gwamna a kan lamurran tsaro, kanal Abdul A Usman mai ritaya.

To sai dai mazauna yankin Sabon Birni sun ce ba wata nasara da suka gani.

Ko bayan wannan, yankin na gabashin Sakkwato ba za'a rasa wasu yankuna ba da har yanzu, matsalar ta rashin tsaro ke addaba, musamman arewa maso yammacin Najeriya, duk da matakan da mahukunta ke dauka na yaki da wannan matsalar.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG