Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Taya Kiristoci Murnar Bikin Ista


Domin murnar zagayowar ranar Ista, Tinubu a cikin sanarwar daya fitar a yau Juma'a, ya bukaci Kiristoci su rungumi halayen kauna da sadaukarwa da tausayin juna da ake dangantawa da wannan lokaci.

WASHINGTON DC - Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Taya Kiristocin Najeriya Dana Duniya Baki Daya Murnar Zagayowar Bikin Ista.

Sanarwar ta ruwaito me magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale yana cewar, Shugaba Tinubu yayi jinjina ga Kiristocin Najeriya dana duniya baki daya a wannan lokaci, inda ya jaddada mahimmancin kauna, sadaukarwa da tausayin juna a matsayin ladubban da lokacin ke koyarwa.

"Shugaba Tinubu ya kara da cewar, sadaukarwa da Yesu Almasihu ya yiwa jinsin dan adam wani darasi ne abun koyi ga shugabanni da ilahrin 'yan Najeriya dake horo akan sadaukarwa da tausayi da juriya a fafutukar samar da dunkulalliyar kasa me cike da zaman lafiya da yalwar arziki."

Tun bayan darewarsa kan karagar mulki a watan mayun bara, gwamnatinsa ta bullo da manufofi da dama da suka yi kyakkyawan tasiri akan al'umma da tattalin arzikin najeriya.

A cewar hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS), a bara, Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur da sanyawa harkar musayar kudade linzami, al'amarin daya sabbaba ninkawar farashin man fetur din har sau 3 da kuma ta'azzarar tsadar rayuwa a yayin da darajar naira tayi mummunar karyewa idan aka kwatanta ta da dalar amurka, sa'annan hauhawar farashin kayan masarufi ta kai kaso 31 .70 cikin 100.

Saidai gwamnatin najeriya mai cin ta sha nanata bukatar 'yan Najeriya su kara juriya game da sauye-sauyen da take kawowa, wadanda tinubu ya bayyana cewar zasu jawo masu zuba jari zuwa kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

A cikin sakonsa na bikin Ista, Shugaba Tinubu ya jinjinawa jumriya da sadaukarwa 'yan Najeriya, inda yace suna da muhimmanci wajen sake farfado da tattalin arzikin kasa.

Ista biki ne da ake gudanarwa domin murnar zagayowar ranar da Yesu Kiristi ya tashi daga matattu.

Kuma wata alama ce dake nuni da samun galabar yesun akan zunubi da mutuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG