Jiya Talata, wasu majiyoyi biyu sun ce matakin gwamnatin Trump na dakatar da ayyukan jinkai a fadin duniya ya hada da dakatar da wani Shirin kungiyar jikan nan na Action Against Hunger, wace take tallafa wa yaran da suke fama da matsalar matsananciyar yunwa a sansanonin ‘yan gudun hijira a kasar Habasha.
Cikin wani sako da aka aike a ranar Asabar, an bayyana wa jami’an asusun tallafin Al’ummar Amurka cewa ana nufin janye duk tallafin da baiwa kasashen waje ne.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, majiyoyin sun bukaci a sakaya sunayen su domin ba a ba su izinin zantawa da ‘yan jarida ba. Wani mai magana da yawun kungiyar agajin jikan ya ki tofa albarkacin bakinsa a game da batun.
Ma’aikatar karkokin wajen Amurka bata amsa sakon kar ta kwanan da aka aike mata ba. Sai dai, wani mai Magana da yawun hukumar ya ranar Lahadi, ya ce akwai bukatar ayi Nazari akan duk ayyukan tallafin da ake bukata a ci gaba da su “domin a tabbatar cewa manufofin su sun dace da manufofin dokokin kasashen wajen Amurka na America First.”
A bara, kungiyar agajin jinkan ta tallafa wa yara 3,000 (dubu uku) masu fama da matsanaciyar matsalar rashin abinci a cewar majiyoyin.
Jimlar mutanen da suka ci gajiyar shirin abincin ta tasam ma mutum 400,000 dake rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke kan iyakar Habasha da kudancin Sudan.
Dandalin Mu Tattauna