Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen M23 Na Congo Na Kara Samun Nasara-Babban Jami'in MDD


M23 Ta Kara Kaimi A Yakinta
M23 Ta Kara Kaimi A Yakinta

A ranar Alhamis ne aka kwashe dakaru a sansanonin sojin Congo da ke lardin Bukavu don karfafa tsaro a wuraren da ke kan hanyar zuwa babban birnin lardin, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Babban jami’in wanzar da zaman lafiya na MDD ya fada a ranar Juma’a cewa ‘yan tawayen M23 suna dannawa zuwa cikin babban birnin lardin Bukavu, bayan kwace ikon garin Goma mai arzikin ma’adanai a gabashin Congo a farkon wannan mako.

“Bayanan da samu na cewa ‘yan tawayen M23 sun dannan da kilomita 60 a arewa da Bukavu. Alamu na nuni da suna dannawa cikin gaggawa,” Jean Pierre Lacroix yana yiwa manema labarai karin bayanai game da ‘yan tawayen masu samun goyon bayan dakarun Rwanda.” Ya ce akwai filin tashi da saukar jiragen sama a inda suke, kuma yana ganin suna kilomitoci kalilan da kudancin Kavumu.

Ya ce idan suka samu nasarar kwace ikon filin saukar jiragen saman kamar yanda suka yi a Goma, toh wannan zai zama wani gagarumin mataki mai muhimmanci.

A ranar Alhamis ne aka kwashe dakaru a sansanonin sojin Congo da ke lardin Bukavu don karfafa tsaro a wuraren da ke kan hanyar zuwa babban birnin lardin, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Shima kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, jami'ai a birnin Bukavu ma suna daukar fararen hula domin su taimakawa wajen kare birnin.

Rwanda ba ta amsa bukatar kamfanin dillancin labaran Reuters nan take ba game da yunkurin soja na baya-bayan nan.

A farkon watan nan ne 'yan tawayen M23 suka rusa yarjejeniyar tsagaita wuta, inda suka kaddamar da wani gagarumin farmaki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tare da goyon bayan sojojin Rwanda. Rwanda dai ta musanta zargin da ake mata na goyon bayan 'yan tawayen.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG