Harin da dakarun RSF suka kai a Kasuwar Sabrein ya kuma jikkata wasu akalla 158, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar a cikin wata sanarwa. Wannan dai shi ne hari na baya bayan nan a jerin munanan hare-haren da aka kai a yakin basasar da ya addabi kasar dake arewa maso gabashin Afirka.
Babu wani bayani kai tsaye daga RSF.
Khalid al-Aleisir, ministan al'adu da na gwamnati, ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa wadanda suka jikkata sun hada da mata da yara da dama. Ya kuma ce harin ya haifar da “barna mai yawa ga kadarorin ‘yan kasuwa masu zaman kansu da na jama’a.”
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce “Wannan laifin na kara nauyin zub da jini kan mayakan.” “Yana zama cin zarafi ga dokokin jin kai na kasa da kasa.”
Kungiyar likitocin Sudan ta yi Allah wadai da harin na RSF. An ce harsashi daya ya kai ‘yan mitoci daga asibitin al-Naw, wanda ya samu mafi yawan wadanda suka jikkata a daga harin kasuwar.
Ta ce akasarin gawarwakin da aka kai asibitin mata ne da kananan yara, inda ta kara da cewa asibitin na da karancin kungiyoyin likitoci musamman likitocin fida da ma’aikatan jinya.
Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023 lokacin da rikici tsakanin shugabannin sojoji da RSF ya barke a babban birnin kasar, Khartoum, da sauran biranen kasar da ke arewa maso gabashin Afirka.
Dandalin Mu Tattauna