Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce ya kai wa tsohon shugaban mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ziyarar gidansa da ke Minna a jihar Neja a ranar Lahadi ne don ya taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A watan Agustan da ya gabata Babangida ya cika shekaru 83 da haihuwa.
Wata sanarwa da Kakakin Obasanjo Kehinde Akinyemi ya fitar a ranar Lahadi ta ce tsohon shugaban bai samu damar zuwa taya IBB murnar wannan biki ba ne saboda ayyuka da suka yi masa yawa kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.
Sanarwar ta kara da cewa, Obansanjo ya kai makamanciyar ziyarar ga Sarkin Benin Esama of Benin, Chief Gabriel Igbinedion, wanda shi kuma ya cika shekaru 90 don taya sa murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Obasanjo ya tarar da tsohon shugaban mulki soji Abdulsalami Abubakar da tsohon mai ba da shwara kan sha’anin tsaron kasa Janar Aliyu Gusau a gidan na IBB kamar yadda ita ma jaridar Leadership ta tabbatar.
Hakan ya sa wasu rahotanni ke nuni da cewa haduwar wadannan kusoshin kasar, ba za ta rasa nasaba da halin da kasa ke ciki ba.
Bayanai sun yi nuni da cewa, shugabannin hudu sun tattauna a kebe har kusan tsawon sa’a guda.
Obasanjo ya ce ba ya kasar ne a lokacin da IBB ya yi bikin cika shekaru 83 a cewar Akinyemi.
Dandalin Mu Tattauna