Kamfanin man fetur din Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewar zai sayar da litar fetur din daya saya daga matatar man dangote akan kudin da bai gaza Naira 950 ba a jihar legas.
A cewar sanarwar, “kamfanin mai na NNPCL ya fitar da jadawalin kiyasin farashin man fetur din da ya sayo daga matatar Dangote a ilahirin gidajen mansa dake fadin kasar.
“Kamfanin NNPCL na bada tabbacin cewar ya sayi man fetur daga matatar Dangote a watan Satumbar da muke ciki a kan farashin kudin dala, kasancewar ba za a fara ciniki da takardar kudin naira ba sai a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa.”
Sanarwar ta kuma kara da cewar mafi kankantar farashin da za a sayar da litar man ba zai gaza Naira 950 a jihar Legas da kewaye.
Ta ci gaba da cewa farashin na iya kaiwa har Naira 1, 019 a jihohi irinsu Borno, kana Abuja, Sokoto, Kano, sauran jihohi kuma za a sayar da shi akan Naira 999, 22.
A yayin da jihohin Oyo da Rivers da sauran sassan kudancin Najeriya, za’a sayar da litar man a kan Naira 950.
Dandalin Mu Tattauna