Hedkwatar Tsaron Najeriya ta ce za a gudanar da bincike kan zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Abbas Haruna har tsawon shekaru shida.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi ta hannun Darektan yada labarai, Birgediya Janar Tukur Gusau, hedkwatar ta ce ta lura da wani bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta inda ake zargin tsare sojan mai mukamin Seaman a rundunar sojin ruwan Najeriya.
A ranar Lahadi aka wayi gari da bullar bidiyon wanda aka dauka a shirin “Brekete Family” mai bibiyar hakkin bil adama da Ahmed Isah yake gabatarwa.
Bidiyon ya nuna yadda matar Abbas Haruna mai suna Hussaina ta zayyana irin halin da mijinta ya shiga bayan da ya samu sabani da shugaban bataliyarsa.
A cewar Hussaina sabanin ya samo asali ne, bayan da mijinta Abbas ya je yin sallah aka zo ba a same shi ba.
Hussaina ta yi ikirarin yadda ta kwashe shekaru shida tana kai komo a tsakanin barikin sojoji da Gombe wajen kokarin ganin an saki mijinta wanda ta ce har haukacewa ya yi sanadiyyar garkame shi da aka yi.
Bidiyon ya janyo kakkausar suka daga sassa daban-daban na Najeriya, inda jama’a suka shiga shafukan sada zumunta suna kira da a bi mata kadinta.
“Muna so mu sanar wa da jama’a cewa, hedkwatar tsaro ta kuduri aniyar tabbatar da adalci da bin doka ta hanyar duba matakan shari’a a kotun soji.
“Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Christopher Gwabin Musa, ya ba da umarni da a gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba kan wannan al’amari. Za mu sanar da jama’a sakamakon wannan bincike a nan gaba.” Sanarwar Birgediya Janar Gusau ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa, “hedkwatar tsaron Najeriya na yin kira ga jama’a da su guji yada bayanan da ba a tabbatar ba yayin da ake gudanar da binciken. Muna masu tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojojin Najeriya za ta gudanar da cikakken bincike bisa adalci.”
Gabanin sanarwar sojojin, wata sanarwa da tsohon mai bai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan sha’anin kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad ya fitar ta ce ya gabatar da wannan al’amari ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Game da batun Hussaina da mijinta, tun jiya na tuntubi ofishin Ministan Tsaro saboda alakar da take tsakaninmu, Minista Dr. Bello Matawalle, ya tabbatar da cewa an sanar da shi kan maganar, kuma tuni ya ba da umarnin a gudanar da bincike nan take.
“Ministan ya kuma tabbatar da cewa za a gudanar da binciken cikin adalci da gaskiya, sannan kuma binciken ba zai dauki lokaci ana gudanar da shi ba.
“Sannan bayan kammala binciken, ina da tabbacin ofishin Ministan zai yi fitar da jawabin yadda sakamakon binciken ya kasance.” In ji Bashir Ahmad.
Dandalin Mu Tattauna