lamarin na faruwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta cire a bara, amma kuma wasu rahotanni ke zargin ana ci gaba da biyan kudin ta bayan fage.
Kudurin kwamatin shi ne a zartar da hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 11 ga watan Yulin bana na ‘yantar da kananan hukumomin daga jihohinsu.
“Sirrin da ke tattare da fannin man fetur din Najeriya da kuma rahotanni da ke cewa kamfanin mai NNPCL na biyan wasu kudade ta wata boyayyiyar hanya don a biya kudin tallafin man, na kara rikitar da mutane.”
“Wannan sabon jirgi da aka sayo a farashi mai rahusa, ya sa Najeriya za ta kauce wa kashe miliyoyin daloli wajen gyara da sayen mai a kowace shekara.” In ji Kakakin Tinubu Bayo Onanuga.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na tuhumar Arabi kan yadda aka sarrafa naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bayar don tallafa wa aikin hajjin 2024.
Wata kungiyar kasar Birtanniya mai suna Savannah Energies ce, mai kokarin samarwa kasashen Afirka wutar lantarki a farashi mai sauki ta soma aikin a garin Mekera na jihar Tahoua.
Fadar shugaban kasar dai ba ta bayyana abin da Tinubu zai je yi a Faransar ba.
Hukumomin Najeriya sun sha musanta cewa an dawo da tallafin man duk da wasu rahotanni da suka nuna cewa gwamnati na biyan kudaden ta bayan fage.
Duk da bugun kirji da tinkaho da wasu gwamnoni a Najeriya ke yi cewa su na gudanar da ayyukan raya kasa, a dayan bangare akwai wasu ayyuka da suke yi wadanda ke sa wasu jama'a kuka saboda asarar da su ke tafkawa.
Iyalai da talakawan daular Gobir da ke Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da zaman zullumi saboda bullar wani faifan bidiyo na basaraken daular da 'yan bindiga suka sace yau fiye da sati uku, su ke ci gaba da barazana ga rayuwarsa da ta dansa da aka sace su tare.
Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce kawo yanzu an sami kamuwa da cutar 39 a bana, a yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar a fadin Afirka.
Wata mummunar ambaliyar ruwa wadda ta biyo bayan ruwan sama masu karfi da aka kwana kuma aka yini ana yi a jihar Zamfara da ke Najeriya ta yi sanadiyyar raba daruruwan mutane da muhallansu tare da hallaka wasu a garin Gummi da wasu kauyukan garin.
Domin Kari
No media source currently available