Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce kawo yanzu an sami kamuwa da cutar 39 a bana, a yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar a fadin Afirka.
Wata mummunar ambaliyar ruwa wadda ta biyo bayan ruwan sama masu karfi da aka kwana kuma aka yini ana yi a jihar Zamfara da ke Najeriya ta yi sanadiyyar raba daruruwan mutane da muhallansu tare da hallaka wasu a garin Gummi da wasu kauyukan garin.
Rikicin na yanzu ya sanya Dubai ta sake amfani da damar domin samun riba, kamar yadda ta yi a lokacin annobar COVID-19 da kuma mamayar Rasha a Ukraine.
“Babu shakka, kamfanin Zhongshan ya boye wasu bayanai ya kuma yaudari kotun Paris wajen ganin an ba shi wadannan jiragen shugaban kasa wadanda suka je kasar ta Faransa don a duba lafiyarsu.” In ji Onanuga.
Majalisar dokokin Najeriya ta bayar da umarnin janye kudirin dokar da ta yi niyyar dakatar da abin da ta kira ayyukan zagon kasa a kasar.
A ranar Laraba, Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kiran a hada taron kwararru don daukan matakan gaggawa kan cutar.
Hukumar kididdiga ta NBS a Najeriya ta ce a cikin watan Yulin shekarar 2024, hauhawar farashin kayayyaki ta sauka zuwa kashi 33.40%.
Ma’aikatar za ta kaddamar da cikakken bincike kan dalilin da ya sa Najeriya ba ta tabuka komai ba a wasannin Olympics da aka kammala a Paris, in ji John Enoh.
“Wannan kudi ba gudunmowa ba ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, kudi ne da hukumar ta kwato ta mika wa gwamnati."
Ginin kotun na daga cikin wuraren da masu boren suka kai wa hari a ranar 1 ga watan Agusta daaka fara zanga-zangar tsadar rayuwa.
Kimanin mutum 500 ne aka tsugunar da su a garin Nguro-Soye da ke karamar hukumar Bama, bayan diban tsawon shekaru da 'yan Boko Haram suka karbi iko da garin.
A ranar Laraba asusun na NELFUND ya fitar da karin jerin jami’o’i, makarantun kimiyya da fasaha da kwalejoji 22 da aka tantance don ba dalibansu bashin karatu
Domin Kari
No media source currently available