Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun hallaka mutum 8 akasarinsu matasa a jihar Nejan Najeriya.
'Yan Najeriya na ci gaba da yin tir da yadda har aka yi 'yan ta'addar daji suka kashe Mai Martaba Sarkin Gobir.
Tuni har tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da al’umar masarautar ta Gobir.
Duk da matsalar karancin mai da tsadar sufuri a Najeriya, yanzu haka an fara samun saukan kayan abinci a kasuwanni daban-daban na kasar, kamar yadda bincike ya nuna a kasuwannin birnin Legas.
lamarin na faruwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta cire a bara, amma kuma wasu rahotanni ke zargin ana ci gaba da biyan kudin ta bayan fage.
Kudurin kwamatin shi ne a zartar da hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 11 ga watan Yulin bana na ‘yantar da kananan hukumomin daga jihohinsu.
“Sirrin da ke tattare da fannin man fetur din Najeriya da kuma rahotanni da ke cewa kamfanin mai NNPCL na biyan wasu kudade ta wata boyayyiyar hanya don a biya kudin tallafin man, na kara rikitar da mutane.”
“Wannan sabon jirgi da aka sayo a farashi mai rahusa, ya sa Najeriya za ta kauce wa kashe miliyoyin daloli wajen gyara da sayen mai a kowace shekara.” In ji Kakakin Tinubu Bayo Onanuga.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na tuhumar Arabi kan yadda aka sarrafa naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bayar don tallafa wa aikin hajjin 2024.
Wata kungiyar kasar Birtanniya mai suna Savannah Energies ce, mai kokarin samarwa kasashen Afirka wutar lantarki a farashi mai sauki ta soma aikin a garin Mekera na jihar Tahoua.
Fadar shugaban kasar dai ba ta bayyana abin da Tinubu zai je yi a Faransar ba.
Domin Kari
No media source currently available