Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Zama Wajibi Tinubu Ya Yi Maza-maza Ya Warware wa 'Yan Najeriya Sarkakiyar Da Ke Tattare  Da Batun Tallafin Mai - Atiku


Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)

“Sirrin da ke tattare da fannin man fetur din Najeriya da kuma rahotanni da ke cewa kamfanin mai NNPCL na biyan wasu kudade ta wata boyayyiyar hanya don a biya kudin tallafin man, na kara rikitar da mutane.”

Tsohon matakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta fito fili ta yi wa al’umar Najeriya karin haske kan rade-radin da ake yi cewa an dawo da biyan tallafin mai.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Atiku ya ce rahotanni sun nuna akasin abin da Tinubu ya fada a jawabin da ya yi wa ‘yan kasa cewa an dakatar da biyan kudin tallafin na mai, yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta fadawa jama’a matsaya guda.

“Wannan rudani tsakanin kalaman Shugaban da abin da yake aikatawa na zubar da kimar shugabancinsa tare da kassara yardar da ke tsakanin jama’a da gwamnati.

“Sirrin da ke tattare da fannin man fetur din Najeriya da kuma rahotanni da ke cewa kamfanin mai NNPCL na biyan wasu kudade ta wata boyayyiyar hanya don a biya kudin tallafin man, na kara rikitar da mutane.” In ji Atiku.

“Idan wadannan rahotanni suka tabbata, za su iya haifar da cikas ga kimar tarrayar Najeriya a matsayin kasa.

“Saboda haka ya zama wajibi gwamnatin Tinubu ta yi maza-maza ta warware sarkakiyar da ke tattare batun tallafin mai da tace danyen mai.” Atiku, wanda ya kara da Tinubu a zaben 2023.

Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce ba ta biyan kudin tallafin mai, amma a ranar Litinin jaridar yanar gizo ta The Cable ta ruwaito cewa Tinubu ya ba NNPCL umarnin ya biya wasu kudade da suka shafi tallafin mai, lamarin da ya haifar da sabon rudani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG