Yayin wannan ziyara, ana sa ran Tinubu zai gana da Shugaban China, Xi Jinping, inda za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi masu muhimmanci a cewar fadar gwamnati.
Sai dai wannan sabuwar kiddiga da hukumar ta NBS ta fitar na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsananciyar tsadar rayuwa, lamarin da ya kai ga gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar a farkon watan Agusta.
Hukumar ta NFF ta sanar cewa ta cimma matsaya da Labbadia dan asalin kasar Jamus, wanda shi ne koci na 37 da zai horar da ‘yan wasan na Najeriya.
Har yanzu ta na kasa ta na dabo game da rikicin 'yan Shi'a da 'yan sandan a Abuja, Najeriya. Hasali ma, 'yan an damke 'yan Shi'a kusan 100 don binciken zakulo masu hannu a kisan 'yan sandan.
A cigaba da nuna bacin rai da kungiyoyi da daidaikun 'yan Najeriya ke yi kan al'amura masu nasaba da rashin tsaro, likitoci matasa sun ja kunnen hukumomi.
Ana ganin wannan karin kudin fasfo a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke korafe korafen tsadar rayuwa, zai haifar da cece kuce. Wasu na iya uzuri ma gwamnati, wasu kuma akasin hakan.
Wata sanarwa da kakakin Tinubu Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, ta ce Ambasada Mohammed Mohammed ne sabon shugaban hukumar ta NIA yayin da Mr. Adeola Oluwatosin Ajayi ya zama sabon Darekta-Janar na hukumar ta DSS.
Likitocin suna kira ne da a ceto Dr. Ganiyat Popoola wacce ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ita a Kaduna sama da watannin takwas da suka gabata.
Wani hari da haramtacciyar kungiyar Shi'a ta Najeriya mai ra'ayin Iran ta kai a babban birnin tarayyar Abuja, ya yi sanadin mutuwar a kalla jami'an tsaro biyu, a cewar 'yan sanda, yayin da wasu uku kuma su ke cikin mawuyacin hali.
Domin Kari
No media source currently available