Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Ayyana Barkewar Annobar Kyandar Biri


Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce kawo yanzu an sami kamuwa da cutar 39 a bana, a yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar a fadin Afirka.

Kimanin sa'o'i 48 bayan hukumar lafiya ta duniya - WHO ta ayyana barkewar annobar kyandar biri a fadin duniya, Najeriya ta shiga cikin shirin ko-ta-kwana.

Hukumomin lafiya na kasar sun ba da sanarwar sabbin kamuwa da cutar, tare da kara nuna damuwa game da karfin kasar na iya shawo kan barkewar cutar, musamman da irin raunin da tsarin kula da lafiyar ta yake da shi.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce kawo yanzu an sami kamuwa da cutar 39 a bana, a yayin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar a fadin Afirka.

Ko da yake ba'a sami rahoton mace-mace a Najeriyar ba, amma bullar kwayar cutar mafi hatsari na da matukar ta da hankali. A halin yanzu jihohin Bayelsa, Cross River, Ogun, da Legas ne suka fi fama da barkewar cutar.

WHO Ta Ce An Samu Cutar Kyandar Biri A Kasashe 12 - Monkey Pox
WHO Ta Ce An Samu Cutar Kyandar Biri A Kasashe 12 - Monkey Pox

Da ya ke jawabi a wani taron manema labarai, shugaban hukumar NCDC Dr. Olajide Idris ya ce al’ummar kasar na kara daukar matakan da suka dace.

Ya ce "wannan taron manema labarai wani bangare ne na kokarin karfafa hadin gwiwa da mu'amala da masu ruwa da tsaki don shawo kan yaduwar cutar da hana shigo da cututtuka."

Cutar ta kyandar biri ta yadu a kasashen Afirka da dama, inda aka sami rahoton kamuwa da cutar sama da 2,800 a cikin kasashe 13 a wannan shekara, tare da asarar rayuka fiye da 500.

Yayin da wani nau'i mai muni ke dada kunno kai, Idris ya bayyana cewa ana duba yiwuwar shirye-shiryen rigakafi ga mutanen da ke da hatsarin gaske.

"Gwamnatin Najeriya na kokarin ganin an samar da alluran rigakafi ga jama'a, musamman ma wuraren da ake fama da munin kamuwa da cutar. An kuma bayyana cewa wadannan alluran rigakafin sun yi tasiri wajen kare lafiyar jama’a, har yanzu ba su iso kasar ba, amma suna kan hanya."

Alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon jiki, rauni, ciwon kai, da kurarraji.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG