A ranar Laraba, Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kiran a hada taron kwararru don daukan matakan gaggawa kan cutar.
Hukumar kididdiga ta NBS a Najeriya ta ce a cikin watan Yulin shekarar 2024, hauhawar farashin kayayyaki ta sauka zuwa kashi 33.40%.
Ma’aikatar za ta kaddamar da cikakken bincike kan dalilin da ya sa Najeriya ba ta tabuka komai ba a wasannin Olympics da aka kammala a Paris, in ji John Enoh.
“Wannan kudi ba gudunmowa ba ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, kudi ne da hukumar ta kwato ta mika wa gwamnati."
Ginin kotun na daga cikin wuraren da masu boren suka kai wa hari a ranar 1 ga watan Agusta daaka fara zanga-zangar tsadar rayuwa.
Kimanin mutum 500 ne aka tsugunar da su a garin Nguro-Soye da ke karamar hukumar Bama, bayan diban tsawon shekaru da 'yan Boko Haram suka karbi iko da garin.
A ranar Laraba asusun na NELFUND ya fitar da karin jerin jami’o’i, makarantun kimiyya da fasaha da kwalejoji 22 da aka tantance don ba dalibansu bashin karatu
A sanarwar da shugaban hukumar Tunji Bello ya fitar, ya ce hukumar na shirin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci a kasar, domin kawo karshen hauhawar farashin kayayyaki da al’ummar ƙasar ke fama da shi.
Kwararru a fannin tattalin arziki sun ce daukan wannan mataki zai taimaka matuka wajen rage hauhawar farashin mai.
"Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambassada Yusuf Tuggar da sauran mambobin majalisar zartarwarsa za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi tare da duba wasu hanyoyi da kasashen biyu za su yaukaka dangatakarsu.”
To sai dai a na ta bangare, hukumar tattara kudade da kayyade su wato RMAFC, cewa ta yi kalaman na tsohon shugaban kasa abin dubawa ne, don haka za ta bi diddigi domin binciko hakikanin gaskiya kan lamarin, tare kuma da yi wa ‘yan kasa cikakken bayani.
Taron majalisar wadda ta kumshi tsofaffin shugabannin kasar da alkalan-alkalai da gwamnonin jihohi, ya tattauna kan zanga-zangar da aka yi da abubuwan da suka haddasa ta da kuma abubuwan da ita ma ta haddasa, musamman a yadda ta rikide zuwa bore a wasu yankuna.
Domin Kari
No media source currently available