Ziyarar ta Tinubu mai shekaru 72, na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a kasar wacce ta fi yawan al’uma da karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Kazalika wannan shi ne taron kasa na farko da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta tun da ya karbi mulki a watan Mayun 2023.
“A dalilin haka, ana umartar jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin walwala a Kaduna da Zaria.” Aruwan ya ce.
Rahotanni daga jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an dage daukacin dokar hana fita a birnin da kewaye.
Harin na zuwa ne yayin da ake ta rade-radin cewa Gwamna Siminalayi Fubara na shirin komawa jam’iyyar ta APP.
Ana ci gaba da aikin ceto rayukan wasu 'yan Najeriya da akalla ba zasu rasa kai goma sha uku ba a wani hadarin jirgin ruwa da ya auku jiya Lahadi a Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.
Wani kazamin rikici da ya barke a tsakanin yan bindiga a Jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 30 daga cikin su, wasu kuma suka samu munanan raunuka.
Gamayyar Kamfanonin Tace Albarkatun Mai a Najeriya (CORAN), sun bayyana cewa har yanzu babu wani memban kungiyar da aka fara sayarwa danyen mai da kudin Naira. Sakataren hulda da jama’a na kungiyar Echie Idoko, ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Mazauna iyakokin Nijar da Najeriya ne a kowane bangare, ke ci gaba da kokawa da matsalolin da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya ta haifar musu.
Ejiogu ya dora alhakin yawaitar hare-hare da ake kaiwa kan masu luwadi da madigo da auren jinsi a Najeriya, da sanya hannu kan yarjejeniyar nan ta Samoa da gwamnatin kasar ta yi.
Gamayyar kamfanonin tace albarkatun mai a Najeriya (CORAN) sun bayyana cewa har yanzu babu wani mamban kungiyarsu da aka fara sayarwa danyen mayi da kudin Naira.
“Saboda haka, bari na fada muku kai-tsaye cewa ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi akwai kuskure a ciki."
Domin Kari
No media source currently available