Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubai Na Kara Cin Gajiyar Rikicin Gabas Ta Tsakiya


A floating restaurant is seen decked up as it is is anchored at Dubai Marina Walk in Dubai, United Arab Emirates, Aug. 13, 2024.
A floating restaurant is seen decked up as it is is anchored at Dubai Marina Walk in Dubai, United Arab Emirates, Aug. 13, 2024.

Yayin da rikici ke dada mamaye yankin Gabas ta Tsakiya, mutane na kara samun arziki a birnin Dubai, da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Tattalin arzikin kasar ta Hamada dai na ci gaba da habaka tare da yawon bude ido da manyan gine-gine, yayin da take a matsayin mafaka a yankin da ke daf da rikicewa, bayan kashe shugaban Hamas Isma'il Haniyeh a Iran.

Zhann Jochinke, babban jami'in hukumar kula da gidaje, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa, "Dubai na cikin wani yanayi na musamman. Mun kasance masu cin gajiyar rikicin yankin, kyakkyawa da mummuna.”

Dubai na da dadadden tarihi na cin gajiyar rikice-rikice a yankin a fakaice. A duk lokacin da hamshakan attajirai suka shiga fargabar tashin hankali, birni yana samar musu da kwanciyar hankali, ƙarancin haraji da tsarin biza mai saukin gaske.

Rikicin na yanzu ya sanya Dubai ta sake amfani da damar domin samun riba, kamar yadda ta yi a lokacin annobar COVID-19 da kuma mamayar Rasha a Ukraine.

UAE-UN-CLIMATE-COP28
UAE-UN-CLIMATE-COP28

Ana kara samun matukar bukata a kasuwar gine-ginen gidaje ta Dubai, da ke kara samar da kadarori masu tsadar gaske.

Kamfanin Emaar Properties mai samun goyon bayan gwamnati, wanda sunansa yake tambari a fadin Dubai, ya sanar da cewa kasuwancinsa na gine-gine ya yi cinikin dala biliyan 8.1 a cikin rabin farko na wannan shekarar, wanda ya karu da dala biliyan 5.2 a daidai wannan lokacin a bara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG