An ta harba gomman hayaki mai sa hawaye ga masu zanga zangar ba tare da la’akari da cewa wata mata na rike da jariri ba.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa talauci da yunwa ya sanya dubban ‘yan kasa daga sassa daban-daban kama hanyar birnin tarayya Abuja, Kaduna, Nasarawa, Sakkwato, Kano, Adamawa, Bauchi, Jigawa da dai sauransu suka hada kai don nunawa gwamnatin yanayin tsananin da ake ciki.
Abubakar Yahaya dan asalin Jihar Katsina da ya fito Zanga-zanga zuwa Eagle Square ya bayyana cewa matakin jefa musu barkonon tsohuwa ba zai dakile su ba.
Mazaunan birnin tarayya Abuja da dama sun bayyana irin yanayin da suka shiga biyo bayan matakin da kwamishinan ‘yan sandan birnin ya dauka na tarwatsa masu zanga-zanga a filin Wasan Moshood Abiola da dandalin eagle square kamar yadda zaku ji a bakin su suna mai cewa bukatunsu basu wuce a dawo da tallafin man fetur, tallafin wutan lantarki, kawo tsaro cikin kasa da dai suransu kamar yadda zaku ji daga bakinsu.
Shi ma masani a sha’anin tsaro, Manjo Mustapha Saliz, mai ritaya ya ce matakin da jami’an tsaro suka dauka a kan masu zanga zanga na harba hayaki mai sa hawaye bai dace ba kuma dole ne a dauki matakan gaggawa wajen biyan bukatun masu zanga-zangar don gudun abun da ka je ya dawo.
A yanzu dai zanga-zangar ya fara daukan salon kona ofis-ofis, fasa shaguna a jihar Kano da ma wasu sassan kasar daban daban lamarin da masana ke cewa kamata ya yi shugaba Tinubu ya yi jawabin kwantar da hankali ga ‘yan kasa kafin abun ya rikide zuwa ga yanayin da ba’a fata kamar yadda aka gani a kasashe irin su Kenya, Sudan da sauransu.
Duk kokarin ji ta bakin jami’an gwamnati kan matakan da za’a dauka a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura ganin yadda muka kira ta wayan tarho da aika sakon kar ta kwana bamu sami martani ba.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna