Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

“Ku Biya Ko Mu Yanke”, Kamfanin AEDC Ya Baiwa Abokan Hulda Wa’adin Sa'o'i 72

Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya
Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin na riko, Victor Ojelabi, ta gargadi kwastomominsa da kodai su biya kudin wutar da suka sha ko kuma ya yanke musu ita.

Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Abuja (AEDC) ya yiwa abokan huldar da suka kasa biyan bashin kudin wutar da yake binsu barazanar yankewa, nan da 3 ga watan Yuni mai kamawa.

Barazanar na kunshe ne a cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin na riko, Victor Ojelabi, ta gargadi kwastomominsa da kodai su biya kudin wutar da suka sha ko kuma ya yanke musu ita.

“Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Abuja na sanarda ilahirin abokan huldarsa da yake bin bashi dasu gaggauta biya domin kaucewa yankewar wuta.

“Don haka, duk kwastoman daya gaza biyan bashin kudin wutar daya sha nan da sa’o’i 72, zuwa Litinin 3 ga watan yuni mai kamawa, zai fuskanci yankewar lantarki.

Kamfanin ya jaddada mahimmancin kiyaye wa’adin biyan kudin wuta, domin samun tafiyar aiki yadda ya dace.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG