A ranar Litiinin Majalisar Dinkin Duniya ta ce, 'yan tawayen M23 sun kaddamar da hare hare a yankin Gabashin Congo inda suka yi garkuwa da a kalla mazaje marasa lafiya da wadanda suka jikkata su 130 daga wasu asibitoci biyu a birnin Goma, a makon da ya gabata.
Shugaban Saliyo wanda ke ziyarar kashin kai a Najeriya ya isa fadar shugaban kasar ne da misalin 12 rana domin yin jinjina ga shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS).
Tawwagar ECOWAS mai shiga tsakani a rikicin siyasar Guinea Bissau ta yi ficewar ba shiri daga birnin Bissau a karshen mako bayan da shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo ya yi barazanar korar tawwagar daga kasarsa
Cikin yanayi mai cike da alhini aka gudanar da jana’izar sojojin Nijar 11 da suka gamu da ajalin su sakamakon wani harin kwanton bauna da wasu 'yan ta’adda masu alaka da kungiyar Al-Qaeda su ka kai musu
Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun musanta a ranar Lahadi cewa an kama wasu mayaka 20 da ke da alaka da kisan kiyashi da aka yi a kasar Rwanda a yankinta, inda suka kira faifan bidiyon na mika su ga Rwanda da cewa “na karya ne.”
Wani mai cutar Ebola na biyu, yaro dan shekara hudu ya mutu a Uganda, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Hukumomin da ke binciken mutuwar akalla mutane 60 a arewa maso yammacin Congo na zargin cewa daya daga cikin tushin ruwa a cikin yankin ya gurbace, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya a ranar Juma'a. Sai dai hukumar ta ce lokaci bai yi ba da za a iya tabbatar da abin da ke faruwa.
Sarkin Musulmin yace za a fara azumin watan Ramadana a Najeriya a gobe Asabar.
“Saka harajin ya zama wajibi, saboda kasashe da dama ba sa kyauta mana, ciki har da kawayenmu da abokan hamayyarmu.” In ji Trump.
Shugabannin ‘yan tawayen na zargin gwamnatin Congo da haddasa fashewar suna masu cewa wadanda suka kai harin na cikin wadanda suka mutu.
“Fiye da rabin al’ummar kasar – mutum miliyan 24.6 – na fuskantar yunwa mai tsanani. Ayyukan kiwon lafiya sun rushe gaba daya. Miliyoyin yara sun shiga rudani kuma an yanke su daga ilimi na hukuma.
Kungiyar kasashen AES da ta kunshi Mali, Nijar da Burkina Faso ta bayyana shirin tattaunawa da kungiyar ECOWAS dangane da yadda za su yi hulda irin ta kungiya da kungiya da nufin tabbatar da dorewar 'yancin walwala da zirga-zirgar al'umominsu a yankin yammacin Afirka baki daya
Domin Kari
No media source currently available