Kwamitin da ya jagoranci babban taron kasa ya mika wa Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar kammalallen rahotonsa makwanni kusan uku bayan zaman da ya tattara daruruwan wakilai
An shiga wuyar mai a biranen Nijar musamman a birnin Yamai inda ake ganin dogayen layin ababen hawa, lamarin da ya haddasa tsaiko a harakokin yau da kullum
A ranar Lahadi, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kai ziyarar wuni guda a Jamhuriyar Nijar, a ci gaba da rangadin da ya kaddamar a kasashen kungiyar AES da nufin karfafa hulda a fannonin da suka hada da diflomasiya, tattalin arziki, yaki da ta'addanci da sauransu.
Wani rahoton cibiyar nazari da bincike ta Institute for Economics and Peace ya ayyana kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso a matsayin yankin Sahel da ya fi ko ina fama da ta'addanci a duniya a shekarar 2024
Yayin da hukumomin Nijar suka rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanin Starlink na Elon Musk domin samar wa kasar ingantacciyar hanyar samun yanar gizo a ko'ina, tare da baiwa duk mai so damar shiga kasar da kayan Starlink bayan biyan harajin kwastam, wannan ya haifar da mahawara a kasar
Trump ya fara jawabinsa ne da cewa "Amurka ta dawo," lamarin da ya haddasa tafi da ihun yabo na "USA! USA!" daga 'yan majalisar jam’iyyar Republican.
A ranar Litiinin Majalisar Dinkin Duniya ta ce, 'yan tawayen M23 sun kaddamar da hare hare a yankin Gabashin Congo inda suka yi garkuwa da a kalla mazaje marasa lafiya da wadanda suka jikkata su 130 daga wasu asibitoci biyu a birnin Goma, a makon da ya gabata.
Shugaban Saliyo wanda ke ziyarar kashin kai a Najeriya ya isa fadar shugaban kasar ne da misalin 12 rana domin yin jinjina ga shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS).
Tawwagar ECOWAS mai shiga tsakani a rikicin siyasar Guinea Bissau ta yi ficewar ba shiri daga birnin Bissau a karshen mako bayan da shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo ya yi barazanar korar tawwagar daga kasarsa
Cikin yanayi mai cike da alhini aka gudanar da jana’izar sojojin Nijar 11 da suka gamu da ajalin su sakamakon wani harin kwanton bauna da wasu 'yan ta’adda masu alaka da kungiyar Al-Qaeda su ka kai musu
Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun musanta a ranar Lahadi cewa an kama wasu mayaka 20 da ke da alaka da kisan kiyashi da aka yi a kasar Rwanda a yankinta, inda suka kira faifan bidiyon na mika su ga Rwanda da cewa “na karya ne.”
Domin Kari
No media source currently available