Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Mutum Na Biyu Da Cutar Ebola Ta Kashe A Uganda


Barkewar cutar Ebola a Uganda
Barkewar cutar Ebola a Uganda

Wani mai cutar Ebola na biyu, yaro dan shekara hudu ya mutu a Uganda, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

Mutuwar ta kawo adadin wadanda aka tabbatar a Uganda zuwa 10.

Kasar dake gabashin Afirka ta ayyana bullar cutar mai saurin yaduwa da yawan gaske a cikin watan Janairu, bayan mutuwar wani ma’aikacin jinya a Asibitin Referral na Mulago da ke Kampala babban birnin kasar.

Ofishin hukumar WHO na Uganda ya buga da yammacin ranar Asabar a kan X cewa, ma'aikatar ta ba da rahoton “samun karin masu kamuwa da cutar, a asibitin Mulago wani mai shekaru hudu da rabi.” Ranar
Talata.

Mulago shi ne babban asibitin da ke kula da masu cutar Ebola a kasar.

Ma'aikatar ta ce a ranar 18 ga watan Fabrairu an sallami dukkan masu fama da cutar Ebola guda takwas da ke karkashin kulawa, amma a kalla mutane 265 sun kasance ana kula da su a Kampala da wasu biranen biyu.

Alamomin cutar Ebola sun hada da zazzabi, ciwon kai da ciwon tsoka. Ana kamuwa da cutar ta hanyar saduwa ko ruwan jikin wanda ya kamu da cutar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG