An kai su makwancinsu ne a wata makabartar Musulmai da ke gabashin garin Agadez
Jana’izar ta samu halartar manyan hafsan sojojin kasar Nijar tare da sauran hukumomi
An kashe sojojin ne a ranar Juma’ar da ta gabata a yankin Ekade Malane da ke jihar Agadez a arewacin Nijar kusa da iyaka da kasar Aljeriya.
Kungiyar ta’addanci da ke da alaka da Al-Qaeda ce ta dauki nauyin kai wannan harin, sai dai masana harkokin tsaro irin su Alkassoum Mato na ganin akwai bukatar gwamnatin Nijar ta sa ke salon yadda take yakar 'yan ta’adda da kuma ba sojojin kasar isassu kayan aiki.
Sojojin Nijar da ke kusa da iyaka da kasar Aljeriya na fuskantar hare-hare daga 'yan bindiga da ke dauke da muggan makamai, lamarin da yassa hukumomi a Agadez ke kira ga al’umma da su ba da gudunmowar da ta dace domin kawo karshen matsalar.
Kasar Nijar da kawayenta na Mali da Burkina Faso sun dai kafa rundunar hadin gwiwa mai dakaru 5000 domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.
Saurari cikakken rahot daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna